Wani mai nazari kan harkokin kudaden kirifto ya yi kira ga mutanen da suke harkar kudaden na intanet da su rage dogon buri.
Adamu Abubakar ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa.
Ya kara da cewa ya yi kiran ne domin kada masu yin wannan harkar su fuskanci karayar zuciya idan ba su samu biyan bukata ba.
A cewarsa, harkar kirifto ba ta da tabbas sannan ana karbar bayanan jama'a da ba su san abin da za a yi da su ba.
Ещё видео!