Dubban magoya bayan juyin mulkin da soja su ka yi a Nijar sun yi gangami jiya Lahadi a wani dandalin wasa da ke Yamai babban birnin kasar domin nuna adawa da wa'adin da kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayar da cewa a sake tare da maido da shugaban kasar da aka zaba a dimokaradiyyance, Mohamed Bazoum, kan karagar mulki.
Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka din ta yi barazanar daukar matakin soji. Sai dai majalisar dattawan Najeriya mai makwabtaka da Najeriya ki goyon bayan shirin, inda ta bukaci Shugaban Najeriya, kuma Shugaban kungiyar ta ECOWAS a ranar Asabar da ya binciko wasu hanyoyin da za a yi amfani da su a maimakon amfani da karfi.
Kungiyar ta ECOWAS dai na iya ci gaba da laluba mafita, dayake akan dau mataki na karshe ne bayan mambobin kungiyar sun cimma jituwa, to amma gargadin da aka yi a jajibirin cikar wa’adin ya haifar da tambayoyi game da makomar batun shiga tsakani. - AP
#voahausa #africa #niger #Nijar #nigercoup #africacoups #MohamedBazoum #Putin #Russia #Rasha #Wagner #deby #Chad #FacebookPage #ECOWAS #AssociatedPress #Bazoum #shorts #short #videoshorts #videoshort
Ku Bibiyi Shafin VOA Hausa YouTube: [ Ссылка ]
- - - - - -
Karin bayani akan VOA Hausa: [ Ссылка ]
Karin bayani akan Facebook: [ Ссылка ]
Karin bayani akan Instagram: [ Ссылка ]
Karin bayani akan Twitter: [ Ссылка ]
Karin bayani akan Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci: [ Ссылка ]
- - - - - -
Shirye-shiryen Sashen Hausa na Muryam Amurka (VOA) wadanda suka hada da na rediyo, talabijin, shafin yanar gizo da kuma kafafen sada zumunta na Facebook, Instagram, Twitter da YouTube, kan kai ga mutum sama da miliyan 17 da ke bibiyar kafar a kasashen Najeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Chadi, Cote d’Ivoire da Jamhuriyar Benin. Sashen kan gabatar da labarai da dumi-duminsu, da batutuwan da suka shafi fashin baki, siyasa, kimiyya, fasahar zamani, kiwon lafiya, kasuwanci da nishadi tare da hadin gwiwar abokanan hulda na gidajen rediyo da talabijin sama da 100 a wasu yankunan Afirka.
Ещё видео!